Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta sanar da cewa, kotun ta biyu na gaban shari'a ta bayar da sammacin kamo shugaban Hibatullah Akhundzada da kuma Abdul Hakim Haqqani, alkalin gwamnatin rikon kwarya na Taliban dangane da halin da ake ciki a Afghanistan. Mutanen biyu suna iko da Afghanistan tun ranar 15 ga Agusta, 2021.
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta ce bisa sakamakon binciken da cibiyar ta yi, akwai dalilai masu ma'ana da za a yarda da cewa wadannan mutane sun aikata laifukan cin zarafin bil'adama ta hanyar "cutarwar jinsi" ta hanyar ba da umarni da tunzurawa, ko kuma karfafa hakan. Wadanda abin ya shafa yaya mata ne da wadanda aka sani da "masu kare mata da 'yan mata".
Kotun ta yi zargin cewa tun bayan da kungiyar Taliban ta karbi mulki, aka aiwatar da tsare-tsare da suka haifar da cin zarafi da cin mutincin bil adama da hana ‘yancin walwala na ‘yan kasar ta Afghanistan. Waɗannan sun haɗa da kisa, tsarewa, azabtarwa, cin zarafi da tilasta bacewa. 'Yan Taliban sun tauye mata da 'yan mata musamman 'yancinsu kamar ilimi, ayyukan sirri, rayuwar iyali, 'yancin walwala, magana, tunani, mazhabin addini.
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta jaddada cewa cin zarafi na jinsi bai takaitu ga ayyukan ta'addanci kai tsaye ba, har ma ya hada da nau'o'in cutarwa na hukumomi da kungiyoyi, gami da sanya ka'idojin zamantakewa na wariya.
A cewar rahoton, duk da zartar da wadannan hukunce-hukunce, kotun ta yanke shawarar boye cikakkun bayanan masu shaidu da wadanda abu ya shafa a halin yanzu don kare lafiyarsu, amma ta yi la'akari da bayyanawa jama'a wannan hukuncin "domin adalci da kuma hana ci gaba da wadannan laifuka".
Your Comment